Takht-Rawanchi: Amurka Ta Yi Kokarin Durkusar Da Gwamnatin Iran Ta Hanyar Takunkuman Tattalin Arziki

2021-01-10 14:23:36
Takht-Rawanchi: Amurka Ta Yi Kokarin Durkusar Da Gwamnatin Iran Ta Hanyar Takunkuman Tattalin Arziki

Jakada sannan wakilin din-di din na kasar Iran a majalisar dinkin duniya (MDD) ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi amfani da takunkuman tattalin arziki don durkusar da gwamnatin kasar tun bayana nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979, kuma har yanzu da alamun za ta ci gaba da amfani da su don cimma manufarta.

Majid Takht-Rawanchi ya bayyana haka ne a lokacinda yake hiri da wasu kafafen yada labarai a birnin New York, ya kuma kara da cewa a baya-bayan nan gwamnatin shugaba Trump ta so ta yi amfani da makaman nukliya kan kasar.

Daga

karshe jakadan ya kara da cewa, a wajen Iran babu babbanci tsakanin jam’iyyu

biyu masu mulkin kasar ta Amurka, Democrat ko Republica. Sai dai a fili yake shugaba

Donal Trump wanda wa’adinsa yak are ya fi muni daga cikinsu.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!