An Kama Shugaban Kungiyar ‘Yan Tawayen Tigray Ta Kasar Habasha
2021-01-10 14:17:13

Majiyar gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa sojojin kasar sun kama shugaban kungiyar yan tawayen Tigray wanda kuma ya samar da kungiyar a yankin tsaunuka na Jihar.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto majiyar sojojin kasar ta Habasha ta cewa an kama shugaban kungiyar Tigray Libration army ne a wani kogo a yankin tsaunuka na arewacin yankin inda ya boye.
Labarin ya kara da cewa sojojin, sun kama tare da shi, wasu mutanen 10 daga cikin jiga-jigan kungiyar ta yantawayen Tigray, har’ila yau da kuma wasu sojojin gwamnatin kasar wadanda suka hadewa yan tawayen.
A lokacin kama wadanan shuwagabannin yan tawayen dai, an yi musayar wuta tare da su, sannan har mutum guda ya rasa ransa.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!