Siriya: An Ga Motocin Amurka 50 Dauke Da Makamai Suna Shiga Lardin Hasaka

2021-01-10 14:14:02
Siriya: An Ga Motocin Amurka 50 Dauke Da Makamai Suna Shiga Lardin Hasaka

Gwamnatin kasar Amurka ta tura motacin daukar makamai 50, dauke da makamai zuwa cikin lardin hasaka na kasar Siriya a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa tawagar motocin har yanzu suna kokarin isa sansanonin sojojin Amurka (yan ta’adda) da suke cikin lardin na Hasaka.

Labarin ya kara da cewa motocin daukar makaman sun shigi kasar ta Siriya ne daga kofar Walid wacce barauniyar hanya ce a wajen gwamnatin kasar.

Amurka dai ta kafa sansanin sojojinta a arewa maso gabacin kasar Siriya ne a shekara ta 2014 ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba, da sunan yaki da kungiyar yan ta’addanci ta Daesh, amma babu abinda take yi sai satar man fetur na kasar da ke yankin na Hasaka.

Masana suna ganin gwamnatin kasar Amurka ce ta samar da kungiyar Daesh a kasashen Siriya da Iraki da nufin mamayar kasashen da kuma rarrabasu saboda maslahar Isra’ila.

19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!