Japan Da Iran Sun Amince Da Aiki Tare Wajen Bunkata Wasanni Da Motsa Jiki A Tsakaninsu

2021-01-10 14:07:13
Japan Da Iran Sun Amince Da Aiki Tare Wajen Bunkata Wasanni Da Motsa Jiki A Tsakaninsu

Ministan wasannin motsa jiki na kasar Iran Masoud Soltanifar ya bada sanarwar cewa an rattaba hannun tsakanin kasarsa da kasar Japan kan yarjejeniyar fahintar juna don bunkasa harkokin wasanni da motsa jiki a tsakanin kasashen biyu.

Jaridar Iran Front Page ta nakalto ministan yana cewa an rattaba hannun ne a wani taro ta kafafen sadarwa na yanar gizo wanda aka gudanar tsakanin sa da ministan wasannin na kasar Japan Kōichi Hagiuda da kuma da kuma jakadan kasar Japan a Tehran Aikawa Kazutoshi.

Ministan wasannin na kasar Iran ta yabawa kasar Japan da yadda ta gudanar da wasannin Olympic a birnin Tokyo na shekara ta 2020 da ta gabata, sannan tana fatan za ta gudanar da wasannin rina mai zuwa, cikin nasara.

.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!