Iran Ta Kirayi Da A Kawo Karshen Irin Goyon Bayan Da Wasu Kasashe Suke Ba Wa Kungiyar Takfiriyya

2021-01-10 09:04:09
Iran Ta Kirayi Da A Kawo Karshen Irin Goyon Bayan Da Wasu Kasashe Suke Ba Wa Kungiyar Takfiriyya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya da Asiya wajen faɗa da ayyukan ta’addanci, tana mai kiran ƙasashen musulmi da su toshe duk wata hanyar da ‘yan ƙungiyar takfiriyya masu kafirta musulmi suke samun taimako da goyon baya.

kakakin Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da yake Allah wadai da kisan gillan da ‘yan ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh suka yi wa wasu haƙar ma’adinai ‘yan ƙasar Pakistan su 11 a lardin Balochistan na ƙasar.

Mr. Khatibzadeh ya ce: Yana da kyau ƙasashen musulmi ta hanyar aiki tare a tsakaninsu su ba da dukkan ƙarfinsu wajen ganin bayan ƙarshen aƙidun da suke share fagen irin waɗannan ayyuka na ta’addanci da kuma kawo ƙarshen duk wata hanya da waɗannan ƙungiyoyi na ta’addanci suke samun kuɗaɗe da taimako.

Har ila yau kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kirayi ƙasashen musulmin da su ɗau matakan da suka dace wajen taimako da goyon bayan da wasu ƙasashe suke ba wa irin waɗannan ƙungiyoyi na ta’addancin.

A kwanakin baya ne dai ‘yan ƙungiyar ta’addancin na Daesh suka kai hari kan masu haƙar ma’adinan mabiyar tafarkin Shi’a Hazara ‘yan tsirarru a yankin a lokacin da suke barci, inda suka tattara su da kai su wani waje suka kashe su.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!