Wani Jirgin Fasinja Ya Bace A Kasar Indonusiya Jim Kadan Bayan Tashinsa

2021-01-10 09:01:38
Wani Jirgin Fasinja Ya Bace A Kasar Indonusiya Jim Kadan Bayan Tashinsa

Rahotanni daga kasar Indonusiya sun bayyana cewar wani jirgin saman fasinja ɗauke da mutane 62 a cikinsa ya ɓace jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin saman birnin Jakarta, babban birnin ƙasar.

Ana tsoron cewa jirgin ƙirar Boeing 737 mallakar kamfanin Sriwijaya Air, ya faɗi cikin kogi ne bayan an daina jin ɗuriyarsa a hanyarsa ta zuwa Pontianak da ke yankin West Kalimantan.

Wasu kafafen watsa labarai dai sun ce akwai kimanin mutane 62 a cikin jirgin da suka hada da wasu yara su bakwai da kuma jarirai 3.

Tuni dai mahukunta a ƙasar suka ce aka baza masu bincike don gano inda jirgin ya ke da ake zaton ya faɗo cikin kogin da ke wajen.

Wasu majiyoyin labarai sun jiyo wasu majiyoyin da abin ya shafa suna cewa an gano burabusan wasu abubuwa da ake zaton na jirgin ne da ya faɗo.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!