Rundunar Sojan Nijeriya Ta Yi Gagarumin Sauyin Wajajen Aiki Ga Manyan Jami’anta

2021-01-10 08:58:36
Rundunar Sojan Nijeriya Ta Yi Gagarumin Sauyin Wajajen Aiki Ga Manyan Jami’anta

A wani gagarumin kwaskwarima, rundunar sojan Nijeriya ta yi sauyin wajajen aiki wa sama da manyan jami’an sojojin ƙasar dubu ciki kuwa har da wasu janar-janar ciki kuwa har da waɗanda suke faɗa da ƙungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram.

Rahotanni sun ce jumular jami’an soji 1,546 ne wannan sauyin ya shafa ciki kuwa har da wasu janar-janar 210, kanar-kanar 450, manjo-manjo 309, Kyaftin-kyaftin 251 da kuma Laftanar-Laftanar 322.

Daga cikin fitattun jami’an sojin da da wannan sauyin ya shafa shi ne Manjo Janar P I Eze wanda aka naɗa a matsayin kwamandan ƙasa na hare-haren nan na Operation Lafiya Dole da suke faɗa da ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a yankunan Arewa Maso Gabashin Nijeriyan.

Wannan sauyin dai ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar take ci gaba da fuskantar matsalar tsaro lamarin da ya sanya da dama suke kiran shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da ya sauya manyan hafsan hafsoshin sojin ƙasar da sauran shugabannin cibiyoyin tsaro na ƙasar.

Shugaba Buharin dai yayi alƙawarin cewa al’ummar ƙasar za su ga sauyi a wannan sabuwar shekarar ta 2021 a ɓangaren tsaron.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!