Read Madrid Ta Fuskanci Koma Baya Wajen Zama Na Daya A La Liga

2021-01-10 08:55:31
Read Madrid Ta Fuskanci Koma Baya Wajen Zama Na Daya A La Liga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fuskanci koma baya a kokarinta na ɗarewa kan teburin gasar League na La Liga na kasar Spain bayan da kungiyar kwallon kafa ta Osasuna ta tilasta mata yin canjaras ba tare da an jefa kwallo a raga ba.

Wasan dai wanda aka buga shi cikin yanayin sanyi mai tsanani ga kuma dusar kankara da take zuba, dukkanin kungiyoyin kwallon kafa sun yi iyakacin kokarinsu wajen zura kwallo amma abin ya ci tura.

A yayin wasan dai ‘yan wasan kungiyar Real Madrid din wato Karim Benzema da kyaftin Sergio Ramos sun sanya kwallo a ragar Osasuna din sai dai kuma alkalin wasan ya hana.

Kungiyar Osasuna din dai wacce ta buga wasanni 11 ba tare da ta yi nasara ba, tana fuskantar kora daga rukunin La Liga na dayan, a daidai lokacin da kungiyar Real Madrid kuma take a matsayi na biyu da maki 37 kasa da kungiyar kwallon kafa ta Atl, Madrid.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!