Iran: Za A Kori Jami’an Hukumar IAEA Daga 21 Ga Fabrairu Matukar Ba A Dauke Takunkumi Kan Iran Ba

Mamba a kwamitin shugabancin
majlaisar dokokin kasar Iran Ahmad Farahani ya bayyana cewa, za a dakatar da dukkanin
ayyuykan bincike na jami’an hukumar IAEA daga ranar 21 ga watan Fabrairu,
matukar dai ba a dauke takunkumai a kan
Iran ba.
A cikin alalam ta bayar da rahoton
cewa, a cikin wani bayaninsa a yau, mamba a kwamitin shugabancin majalisar
dokokin kasar Iran Ahmad Farahani ya bayyana cewa; tun bayan da Iran ta rattaba
hannu kan yarjejeniyar nukiliya bangare ne daya ne yake aiki da wannan
yarjejeniya shi ne Iran.
Ya ce wannan ba abu ne mai yiwuwa
ba, domin kuwa aiki da dukkanin bangarorin yarjejeniyar yana akan dukkanin
wadanda suka rattaba hannu a kanta ne, dukkanin kasashen turai ba su aiki da ko
daya daga cikin alkawullansu ba, kamar yadda Donald Trump ya ma fitar da Amurka
daga cikin yarjejeniyar ne baki daya.
Farahani ya ce; zababben shugaban
kasar Amurka yana wata daya cikakke daga ranar da za a rantsar da shi kan ya
janye dukkanin takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran, a bangarori na tattalin
arziki, kasuwanci, musayar kudade, cinikin mai da sauransu, idan kuma bah aka ba,
aikin hukumar makamashin nukiliya ta duniya ya kawo karshe a cikin cibiyoyin
nukiliya na kasar Iran.
Ya kuma kara da cewa, wannan kudiri
na majalisa dole ne gwamnatin Iran ta aiwatar da shi daga ranar da aka ayyana.
015