​Biden: Rashin Halartar Trump A Wurin Taron Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka Abu Ne Mai Kyau

2021-01-09 19:46:16
​Biden: Rashin Halartar Trump A Wurin Taron Rantsar Da Sabon Shugaban Amurka Abu Ne Mai Kyau

Zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden ya mayar da martani kan furucin Donald Trump na cewa ba zai halarci taron rantsar da sabon shugaban kasa ba, da cewa hakan abu ne mai kyau.

Joe Biden ya bayyana cewa, rashin halartar Trump a wurin rantsar da shi ya fi alhairi, domin kuwa shi Trump mutum ne da ya jawo wa Amurka abin kunya a idon duniya, tare da tozarta matsayinta.

Haka nan kuma Biden ya bayyana cewa, ba a taba samun wani shugaba a kasar Amurka mafi muni kamar Trump ba, saboda a lokacinsa ne aka keta alfarmar demokradiyya a Amurka tare da umarninsa.

A daya bangaren kuma Joe Biden ya yaba da matakin mataimakin Trump Mike Pence ya dauka, na kin amincewa da salon siyasar tayar da tarzoma da Trump ya dauka a cikin kwanakin nan, musamman yadda ya tunzura magoya bayansa suka kaddamar da farmaki kan majalisar dokokin Amurka.

Yanzu haka dai wasu bayanai daga kasar ta Amurka na cewa, akwai yiwuwar Mike Pence mataimakin Donald Trump ya zama shi ne zai mika mulki ga zababben shugaban kasar ta Amurka, bayan da Trump ya ce ba zai halarci wurin ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!