​Iran Ta Dakatar Da Sayen Rigakafin COVID-19 Na Kamfanin Pfizer Bayan Haramcin Hakan Da Jagora Ya Sanar

2021-01-09 17:17:56
​Iran Ta Dakatar Da Sayen Rigakafin COVID-19 Na Kamfanin Pfizer Bayan Haramcin Hakan Da Jagora Ya Sanar

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Iran ta sanar da cewa an dakatar da sayo rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer na Amurka ya samar bayan haramcin hakan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sanar cikin wani jawabi da yayi a jiya.

Kakakin kungiyar Mohammad Hasan Qosian Moqaddam ne ya sanar da hakan a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Iran IRNA an dakatar da sayo allura 150,000 na rigakafin da kamfanin na Pfizer ya samar wanda a baya kungiyar ta ke shirin sayowa daga Amurkan.

Jami’in ya kara da cewa a halin yanzu suna shirin sayo rigakafin daga wasu kasashen na Gabashi idan har bukatar hakan ta taso.

A jiya Juma’a ce dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana rashin amincewarsa da sayo rigakafin cutar COVID-19 din daga kamfanonin Amurka da Birtaniyya yana mai cewa: Idan da Amurkawa sun iya samar da rigakafin, toh da kuwa ba su fuskanci irin wannan mummunan yanayi da suke ciki ba. Jagoran ya ce shi dai hankalinsa bai kwanta da su ba, don kuwa a wasu lokuta suna son ne su gwada rigakafin na su a kan wasu al’ummomi.

Sai dai Jagoran ya ce gwamnatin kasar ta Iran tana iya sayo rigakafin daga wani wajen na daban wanda ake da tabbaci kansa.


015


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!