Mali: Tsohon Firayi Minista Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Bai Gudu Ba –Lauya

Lauyan tsohon firayi ministan kasar Mali Boubou Cisse da ake zargi da hannu cikin makarkashiyar kifar da gwamnatin rikon kwarya ta kasar ya musanta cewa tsohon firayi ministan ya gudu daga kasar bayan da babban mai shigar da kara na kasar ya zarge shi da kokarin juyin mulkin.
A ranar 31 ga watan Disamban da ta gabata ce mai shigar da karar ya
bayyana cewar ana gudanar da bincike kan wasu mutane bakwai ciki kuwa har da
tsohon firayi minista Cisse saboda zargin kulla makarkashiya ga gwamnatin rikon
kwaryar, inda ya ce biyar daga cikinsu suna tsare amma shi firayi ministan ya
tsere.
Yayin da yake mayar da martani kan wannan ikirarin, daya daga cikin
lauyoyin Mr. Cissen, Marcel Ceccaldi ya bayyana wa manema labarai cewa wanda
yake wakiltan yana nan a birnin Bamalo kuma cikin koshin lafiya.
Shi ma a nasa bangaren Mr. Cisse, a wata hira da yayi da gidan
radiyon Jamus ya ce yana nan a kasar Mali sai dai bai fadi inda yake ba, yana
mai cewa jami’an tsaro sun zo gidansa a lokacin ba yana nan inda suka ci
zarafin mutanen da suke gidan, wanda hakan ya sanya ne neman mafaka.
A ranar 18 ga watan Augustan da ya gabata ne dai sojoji suka kifar
da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita sakamakon rikicin
siyasar da ya kunno kai a kasar, sai dai kuma sakamakon matsin lamba sojojin
sun mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta kasar.
015