​Kim: Amurka Ita Ce Babbar Makiyar Koriya Ta Arewa Ko Waye Kuwa Ke Shugabantar Kasar

2021-01-09 16:37:41
​Kim: Amurka Ita Ce Babbar Makiyar Koriya Ta Arewa Ko Waye Kuwa Ke Shugabantar Kasar

Shugaban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya bayyana cewar Amurka dai ita ce babbar abokiyar gabar kasarsa yana mai cewa siyasar kiyayyar da Amurka take aiwatarwa kan Koriya ta arewa ba za ta sauya ba ko waye kuwa yake shugabancin Amurkan.

Shugaba Kim Jong-un ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a wajen babban taron jam’iyya mai mulki a kasar a yau din nan Asabar ‘yan kwanaki kafin a rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban Amurkan inda ya ce daya daga cikin abubuwan da za su tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Koriya ta arewa shi ne yin watsi daga wannan siyasar ta kiyayya da kasar da Amurka take yi.

Shugaba Kim ya ce: Ko ma wane ne a kan karagar mulkin Amurka yanayi siyasar Amurka a kan kasar Koriya ta arewa ba zai sauya ba, yana mai shan alwashin kara karfafa alaka da dukkanin kasashen da suke adawa da mulkin mallakan manyan kasashen duniya irin su Amurka.

A wani bangare na jawabin nasa shugaba Kim ya bukaci jami’an kasar da su kara kaimi wajen ci gaba da samar da makamai da kuma fasahohin da za su kara karfin da kasarsa take da shi ciki kuwa har da kara kera makamai masu linzami masu cin dogon zango da kuma jiragen sama marasa matuka na leken asiri; kamar yadda kuma ya kara kiran da a kara karfafa makaman nukiliyan da kasar take da su don mayar da martani ga barazanar da kasarsa take fuskanta.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!