​MDD: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake A Kamaru

2021-01-09 16:22:40
​MDD: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake A Kamaru

Wata mace ‘yar kunar bakin wake ta kashe mutane 13 a arewacin kasar Kamaru bayan da ta tayar da bama-baman da ta yi jigida da su cikin wasu mutanen da suke gudun tsiratar da rayukansu daga hare-haren wasu ‘yan bindiga dadi.

A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da jama’a suka tarwatse bayan da wasu mahara suka kai hari garin Mozogo da ke yankin Arewa mai nisa na kasar Kamarun kusa da kan iyaka da Nijeriya inda a irin wannan yanayin ne wata mace wacce take dauke da ababe masu fashewar ta tarwatsa kanta a cikin jama’an.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhalin kai wannan harin wanda daga cikin wadanda suka rasa rayukan na su har da mata da kananan yara, sai dai ana nuna yatsar zargi ga kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram wacce take kai irin wadannan hare-hare a yankin.

Wadannan hare-haren dai suna zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ta’addanci ke kara karuwa a yankin duk kuwa da kasantuwar sojojin waje musamman na Faransa a yankin wanda wasu suke zargi da hannu cikin goyon bayan wasu kungiyoyin ta’addanci.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!