Sayyid Nasarallah:Amurkawa Sun Gano Hatsarin Trump A Baya-Bayan Nan

2021-01-09 10:24:17
Sayyid Nasarallah:Amurkawa Sun Gano Hatsarin Trump A Baya-Bayan Nan

Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a birnin washington na kasar Amurka a ranar Laraban da ta gabata sun bayyana hakikanin yadda democradiyyar Amurka take.Kamfanin dillancin labaran Nisim na kasar Iran ya nakalto sayyeed Nasarallah yana fadar haka a jiya jumma’a da yamma, a lokacinda yake jawabi a tashar talabijin ta kungiyar a birnin Beirut.

Sayyeed nasarallah ya kara da cewa duk kokarinda kawayen Amurka a yankin suka yi na nuna cewa mamayar majalisar dattawan kasar Amurka wanda magoya bayan Trump suka yi ba kome bane, sai dai mafi yawan kasashen duniya sun fahinci cewa akwai matsaloli da dama a cikin siyasar kasar Amurka. Kuma abinda aka gani ranar Laraba kasan ne daga ciki..

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!