Najeriya: Sojoji Sun Ce Suna Ci Gaba Da Fatattakar Boko Haram A Borno

2021-01-09 10:15:20
Najeriya: Sojoji Sun Ce Suna Ci Gaba Da Fatattakar Boko Haram A Borno

Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta ce; ta lalata akalla motocin bindiga 2 na ‘yan ta’addan Boko Haram, tare da kakkabe wasu da dama daga cikin mayakansu a hanyar Wamdeo-Chul na yankin Kudancin jihar Borno. Jaridar Leadership ta Hausa a shafinta na yanar gizo ta kara da cewa .

Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon da ya gabata.

Ya kuma kara da cewa an cimma wannan nasarar ne a ranar, 5 ga Janairun 2021, a yayin da dakarun suka hada hannu da jiragen yaki masu saukar ungulu na NAF don basu tallafi ta sama yayin da suke kokarin fatattakar ‘yan ta’addan, wadanda suka yi yunkurin keta wuraren 2.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!