Kungiyar Persepolis A Shirye Take Don Shiga Gasar AFC
2021-01-09 09:39:08

Kungiyar kwallon kafa ta Persepolis a nan Iran a shirye take ta shiga wasan karshe na daukar kofin AFC a yau asabar, a karawarta da Ulsan Hyundai a filin wasanni na Al-Janoub dake birnin Doha na kasar Qatar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kungiyar ta yi kokari a wasanninta a group C, inda ta sami nasara a dukkanin wasanninta, in banda guda. Wanda kuma ya bada damar zama zakara a group din.
Wannan shi ne karo na biyu kenan wanda kungiyar take kaiwa wasan karshe ba tare da daukar kofi ba.
Ana saran a wasan na yau zata sami sa’ar daukar kofin. A wasanta na karshe da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Al-nassraa ta kasar Saudiya, ta lallasata a bugun daga kai sai gola.
Tags:
persepolis
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!