‘Yan Jam’iyyar Democrats Na Amurka Na Shirin Tsige Shugaba Trump Daga Mulki

2021-01-08 14:16:54
‘Yan Jam’iyyar Democrats Na Amurka Na Shirin Tsige Shugaba Trump Daga Mulki

‘Yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyar Democrats suna ci gaba da ƙoƙarin da suka faro tun shekaran jiya na tsige shugaban ƙasar Donald Trump kwanaki biyu bayan ya sake ikirarin an tabka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar da kuma tunzura magoya bayansa da su mamaye majalisar.

Manyan jagororin jam’iyyar Democrats ɗin da suka haɗa kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi da shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin Chuck Schumer sun yi kira da a fara gudanar da shirye-shiryen tsige Trump ɗin matuƙar mataimakin shugaban ƙasar Mike Pence da sauran ministocin gwamnatin Trump ɗin ba su ɗau matakan tuɓe daga karagar mulki ɗin ba.

Cikin wata sanarwar da suka fitar a jiya Alhamis sun ce ayyukan cin amana da shugaba Trump ɗin ya aikata sun wajabta gaggauta korarsa daga mulki.

Sakamakon ci gaba da kiran a tuɓe shi daga mulkin, a jiyan dai Trump ya fitar da wani faifan bidiyo inda yayi Allah wadai da tarzomar da ta ɓarken da tayi sanadiyyar mutuwar alal aƙalla mutane huɗu, sai dai kuma wasu suna ganin hakan ba zai iya wanke shi daga hannun da yake da shi cikin wannan rikicin ba.

To sai dai kuma bisa la’akari da kasa da makonni biyu kenan da Trump ɗin zai bar mulki sakamakon kayen da ya sha a zaɓen shugaban ƙasar, ana ganin da wuya ‘yan Democrats ɗin su sami cikakken lokacin da ake buƙata wajen tsige shi ɗin, to sai dai duk da hakan Trump ɗin zai shiga cikin tarihi a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin Amurka da ya haifar da kace-nace sosai a ƙasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!