Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Nuna Wani Sansanin Makamansu Masu Linzami Na Karƙashin Kasa

Dakarun
kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran sun nuna wani ɓangare na wani
sansanin makamansu masu linzami na ƙarƙashin ƙasa da ke wani wajen da ba a
tantance ko ina ba ne, a daidai lokacin da kai ruwa rana tsakanin Iran da
Amurka ke ci gaba da ƙamari.
Yayin
yake ƙarin bayani kan wannan wajen wanda gidan talabijin ɗin ƙasar ya nuna shi,
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Hossein
Salami ya bayyana cewar sansanin dai ɗaya ne daga cikin sansanonin da sojojin
ruwa na dakarun kare juyin Musulunci suke ajiye da makamansu masu linzami.
Janar
Salami ya ce makamai masu linzamin da aka jibge su a wajen suna cin zango na ɗaruruwan
kilomitoci ne kuma suna da ƙarfi tarwatsa duk wani wajen da ake so su tarwatsa
kamar yadda kuma suna iya tsira daga ganowa ko kuma tarwatsawar makaman maƙiya.
Babban
kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa makamai masu
linzamin da sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka
mallaka suna daga cikin makamai masu linazami na zamani kuma masu karfin gaske
da za a iya amfani da su daga doron kasa zuwa cikin teku, sannan daga teku zuwa
teku, daga doron ƙasa zuwa doron ƙasa sannan daga sama zuwa teku.
Janar
Salami ya ci gaba da cewa a duk lokacin da buƙatar amfani da waɗannan makamai
ta taso Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi ƙasa a gwuiwa wajen kare kanta
ba.
A shekarar da ta gabata ce dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka sanar da ƙera wani ‘birnin makamai masu linzami’ suna masu jan kunne maƙiya da kada su bari wani gigi ya ɗebe su su kawo wa ƙasar hari.