Gwamnatin Nijeriya Ta Ba Da Umurnin Da A Dakatar Da Aiki Da Sabon Farashin Wutar Lantarki A Kasar

2021-01-08 14:05:58
Gwamnatin Nijeriya Ta Ba Da Umurnin Da A Dakatar Da Aiki Da Sabon Farashin Wutar Lantarki A Kasar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ba wa Hukumar kula da farashin wutar lantarki ta ƙasar wato Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) umurnin da ta dakatar da fara aiki da sabon farashin wutar lantarkin da ta sanar a kwanakin baya, ta ci gaba da aiki da yadda farashin da aka tsayar a watan Disamban 2020.

Kafar watsa labaran nan ta Premium Times ta buga labarin cewa ministan makamashi na Nijeriyan, Saleh Mamman ne ya ba da umurnin a jiya Alhamis inda ya buƙace hukumar da ta koma ga yadda farashin yake a watan Disambar shekarar bara.

Yayin da ya ke sanar da hakan, babban mai ba wa ministan shawara kan harkokin watsa labarai, Aaron Artimas, ya ce ministan ya ɗau wannan matakin ne don taimakawa wajen cimma yarjejeniyar da ta dace a ci gaba da tattaunawar da ake da ƙungiyoyin kwadago kan lamarin.

Ministan dai yana mayar da martani ne kan rahotannin da suke cewa Hukumar kula da farashin wutar lantarki ta Nijeriyan ta ƙara farashin wutar lantarkin da kashi 50 cikin ɗari lamarin da ya sake janyo kace-nace a ƙasar musamman idan aka yi la’akari da cewa ba a jima da ƙara farashin wutar lantarkin ba, sannan kuma ga matsaloli na rayuwa da al’ummar Nijeriyan suke fuskanta.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!