Rouhani: Zanga-Zangar Amurka Alama Ce Ta Rushewar Demokradiyyar Yammaci

2021-01-07 21:03:39
Rouhani: Zanga-Zangar Amurka Alama Ce Ta Rushewar Demokradiyyar Yammaci

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar tarzomar da magoya bayan shugaba Trump suka haifar yayin tabbatar da sakamakon zaben Amurka a majalisar kasar wata alama ce dake nuni da raunin demokradiyyar kashashen Yammaci da kuma rushewarta.

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi yayin bude wasu ayyukan ci gaban kasa inda yayin da yake magana kan abubuwan da ke faruwa a Amurkan ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne mun ga yadda siyasar amfani da tunzura mutane ta yi kauri a wadannan kasashen don cimma wata manufa ta siyasa, shugaban yana ishara ne da yadda shugaban Amurka ya yi kokarin tunzura mutane wajen haifar da fitina.

Shugaban na Iran ya kara cewa da cewa duniya dai ta shaidi irin yadda shugaba Trump ya cutar da kasar Amurka da kuma haifar mata da wulakanci cikin shekaru hudun da suka gabata kamar yadda kuma ya haifar da hasarori da cutarwa ga al’ummomin yankin Gabas ta tsakiya, a Falastinu, Siriya da kuma Yemen.

Shugaba Rouhani ne ya ce hakan shi ne sakamakon da za a iya fuskanta matukar wani mutum mara kwarewa wanda kuma bai dace ba ya dare karagar mulkin wata kasa, ta yadda zai cutar da kasarsa da kuma sauran kasashen duniya.

Don haka sai shugaba Rouahanin ya ce yana faran hakan zai zamanto darasi da dukkanin duniya da kuma shugabannin Amurkan masu zuwa.

A jiya ne dai magoya bayan shugaba Trump suka fada wa majalisar Amurkan a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zama inda ‘yan majalisar za su tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban 2020 wanda dan takarar jam’iyyar Democrats Joe Biden ya lashe amma Trump din ya ki amincewa da sakamakon.

Alal akalla mutane hudu ne dai suka rasa rayukansu yayin wannan tarzomar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!