Manyan Jami’an Amurka Sun Fara Murabus Tun Bayan Harin Da Magoya Bayan Trump Suka Kai Majalisa

2021-01-07 21:00:15
Manyan Jami’an Amurka Sun Fara Murabus Tun Bayan Harin Da Magoya Bayan Trump Suka Kai Majalisa

Rahotanni daga Amurka sun bayyana cewar wasu manyan jami’an fadar White House ta Amurka sun fara mika takardun murabus din su daga mukaminsu don nuna rashin jin dadinsu da yadda shugaba Trump din ya tunzura da kuma goyon bayan magoya bayansa da suka kai hari majalisar kasar a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaman tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Rahotannin sun ce daga cikin jami’an da ya yi murabus din shi ne Mattwe Pottinger, mataimakin babban mai ba wa shugaba Trump din shawarar kan harkokin tsaro wanda ya mika takardar murabus din na sa tun a jiya Laraba.

Rahotannin dai sun ce Mr. Pottinger yayi murabus din ne saboda rashin jin dadin yadda Trump yayi amfani da magoya bayansa wajen haifar da tarzoma a kasar.

Har ila yau wasu majiyoyin sun ce hatta shi kansa babban mai ba wa shugaban kasa shawarar kan harkokin tsaron Robert O’Brien yana tunanin yin murabus din da barin fadar ta White House, sai dai kuma wasu na kurkusa da shi suna kiransa da ya ci gaba da zama.

Har ila yau daga cikin wadanda ake maganar suna shirin yin murabus din sun hada da Chris Liddel mai bawa shugaban kasa shawara kana kuma mataimakin shugaban ma’aikata na fadar White House din. Har ila yau shugabar ma’aikatan matar shugaban Amurkan ma Stephanie Grisham ita ma tana shirin mika takardar murabus din nata.

A ranar Larabar nan ne dai shugaba Trump din ya karfafa magoya bayansa inda suka kai hari da kuma mamaye majalisar kasar a lokacin da ake shirin gudanar da zama don tababtar da sakamakon zaben shugaban kasar da Joe Bide na jam’iyyar Democrats ya lashe, lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniya da kuma tabbatar da rashin ingancin ikirarin Amurka na riko da tsarin demokradiyya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!