WHO Ta Bukaci A Dau Matakan Gaggawa Wajen Dakile Bullar Sabuwar Cutar Corona A Turai

2021-01-07 20:49:57
WHO Ta Bukaci A Dau Matakan Gaggawa Wajen Dakile Bullar Sabuwar Cutar Corona A Turai

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) reshen kasashen Turai ta bayyana cewar akwai bukatar a kara kaimi sosai wajen fada da sabuwar cutar nan ta Coronavirus da ta kunno kai a kasashen Turan da kuma suka fara barazana ga duniya.

Babban daraktan hukumar ta WHO reshen Turai Hans Kluge ne ya bayyana hakan a wani jawabi da yayi inda ya bayyana halin da ake ciki a halin yanzun da cewa wani yanayi ne mai tada hankali cikin yanayin annobar da ta sake bullowa a Turai.

Mr. Kluge ya ci gaba da cewa: Wannan wani yanayi ne mai tada hankali, wanda hakan ke nuni da cewa wajibi ne mu yi aiki tukuru cikin karamin lokaci wajen daukan matakan kiwon lafiya da na zamantakewar al’umma don dakile wannan cutar da aka fara gano ta a Ingila.

Matakan da jami’in ya ce a kara ba su muhimmancin sun hada da irin wadanda dama ake magana a kansu da suka hada da sanya takunkumin rufe baki da hanci, ba da tazara wajen wani taro, wanke hannaye da dai sauransu wanda ya ce akwai bukatar a kara ba su muhimmanci, tare kuma da gudanar da gwaji da kuma yin rigakafin cutar.

Hukumar WHO din reshen Turai ta kumshi kasashe 53 da suka hada da dukkanin kasashen Turan da Rasha da wasu kasashen tsakiyar Asiya da sauransu, kuma bullar cutar coronan ta yi musu illa da kuma haifar da mutuwa sama da shekarun da suka gabata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!