​Amurka: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar Da Joe Biden A Matsayin Zababben Shugaban Kasa

2021-01-07 15:03:45
​Amurka: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar Da Joe Biden A Matsayin Zababben Shugaban Kasa

Rahotanni daga kasar Amurka sun tabbatar da cewa, majalisar dokokin kasar ta tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaba kasar a hukumance, bayan da majalisar ta ci gaba da zamanta, biyo bayan farmakin da magoya bayan Trump suka kaddamar kan majalisar, inda suka hana majalisar gudanar da zama.

Mutane 4 aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon tarzomar da magoya bayan Donald Trump suka tayar a cikin ginin majalisar dokokin kasar a birnin Washington, a lokacin da ‘yan majalisar ke gudanar da zama domin tabbatar da nasar nasarar Joe Biden.

Farmakin magoya bayan Trump dai ya tilasta majalisar dakatar da zaman da take gudanarwa dangane da sakamakon zabe, inda Trump din ya rika zuga su da kuma tunzura su domin su kawo cikas ga zaman, wanda ya yi imanin cewa za a tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashen shugaban kasar da aka gudanar.

Daga bisani bayan da jami’an tsaro suka samu nasarar fitar da masu tarzomar, majalisar ta ci gaba da gudanar da zamanta.

Kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da abin da ya faru, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin dimukradiyya, tare da kira ga bangarorin da suka sha kayi a zaben da amince da shan kayin da suka yi, maimkaon tayar da tarzoma.

A nasa bangaren zababben shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya bayyana abin da yake faruwa da cewa, hari ne aka kaddamar kan dimukradiyyar Amurka.

Shugabannin kasashen arewaci da kudancin Amurka duk sun yi Allawadai da kakkausar murya kan abin da Doald Trump da magoya bayansa suka yi.

Sakamakon abin da ya faru a daren jiya, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin sun yi murabus daga kan mukamansu domin nuna rashin amincewarsu da abin da ya aikata, daga ciki har da babbar sakatariyar hulda da jama’a ta fadar White House.

Za a ranatsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban kasar Amurka aranar 20 ga wannan wata na Janairu da muke ciki na shekarar 2021.

Bayan matakin majalisa na amincewa da Biden a hukumancea matsayin wanda ya lashe zabe, a yau Trump ya ce zai amince ya mika mulki ta hanyoyi na lumana.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!