Iran: Dakarun BASIJ Sun Fara Gudanar Da Atisaye A Cikin Tekun Fasha

2021-01-07 14:59:23
Iran: Dakarun BASIJ Sun Fara Gudanar Da Atisaye A Cikin Tekun Fasha

Dakarun sa kai na Basij na kasar Iran sun fara gudanar da wani gagarumin atisayi a cikin tekun fasha, da jiragen ruwa na yaki guda 700.

Rahotanni sun ce dakarun na Basij sun fara gudaar da wannan atisayi nea yau Alhamis daga gabar ruwan kasar Iran ta Bandar Abbas, inda suke sintiri da gwada makamai a cikin jiragen ruwa na yaki guda 700.

Wannan atisayin dai yana zuwa nea daidai lokacin da zaman dar-dar ke karuwa a yankin, sakamakon barazanar da makiyan kasar ta Iran suke yi a kanta.

A cikin wanann makon da ya gabata ne Amurka ta aike da babban jirgin ruwa da ke dauke da jiragen yaki zuwa cikin tekun fasha, wanda kuma hakan na zuwa ne a lokacin da wasu bayanai na sirri ke ishara da cewa, mai yiwuwa Donald Trump ya gigin kaddamar da hari kan Iran kafin ya bar mulkin Amurka.

A nasa bangaren babban kwamandan dakarun IRGC na Iran Janar Hussain Salami ya bayyana cewa, sun kammala dukkanin shirinsu domin tunkarar kowace irin barazana daga makiya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!