Amurka : Magoya Bayan Trump, Sun Afka Wa Majalisar Dokoki

2021-01-07 10:16:56
Amurka : Magoya Bayan Trump, Sun Afka Wa Majalisar Dokoki

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da harin da magoya bayan shugaba mai barin gado na Amurka suka yi a majalisar dokokin kasar a lokacin da ‘yan majalisar kasar ke taro domin tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar democrat Joe Biden.

Lamarin dai ya haifar da rikici tsakanin magoya bayan Trump, da kuma ‘yan sanda wanda ya haifar da tarzoma a ginin majalisar wato capitol a jiya Laraba.

Kasashen duniya da dama musamman manyan kawayen Amurka na turai, duk sun nuna jin takaici game da lamarin, wanda suka ce tamakar yi wa tsarin demokuradiyar Amurka karan tsaye ne.

Baya ga hakan manyan jami’an Amurka da ‘yan siyasa da kuma tsoffin shugabannin kasar irin su Bill Clinton, da Barack Obama duk sun yi tir da lamarin.

Shafukan sada zumunta na twitter da facebook, su ma sun dakatar da shafukan Trump na wani dan lokaci, saboda abin da suka kira karya dokokinsu.

Rahotanni daga Amurkar sun ce an samu hasarar rayuka yayin tarzomar.

Daga bisani dai majalisar dokokin ta Amurka ta koma zama domin ci gaba da tattaunawar hadin gwiwa domin tabbatar da nasarar Joe Biden.

Trump dai ya shafe makonni yana ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben kasar, inda ya ce an yi magudi a manyan jihohin da Biden ya yi nasara ba tare da ya gabatar da wata hujja ba.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!