Iran : Ba Zamu Taba Mika Kai Ba Bisa Matsin Lamba

2021-01-07 10:12:23
Iran : Ba Zamu Taba Mika Kai Ba Bisa Matsin Lamba

Shugaban Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Hassan Rohani, ya bayyana cewa kasarsa ba zata taba mika kai ba bisa matsin lamba ba.

Don haka Iran, tana maraba da duk wani mataki da sabuwar gwamnatin Amurka za ta dauka bisa mutunci da doka da kuma cika alkawura.

Ta hakan ne ita ma Iran, za ta cika alkawuranta, kamar yadda shugaban kasar Hassan Rohani ya bayyana yayin taron majalisar ministocinsa.

A cewar Rohanin, idan har AMurka ta cika duka alkawuran data dauka, ta Iran za ta mutunta na ta alkawuran gabadaya, amma ba zamu taba mika kai bag a matsin lamba, inji shugaba Rohanin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!