Tababa Kan Harin Da Ya Yi sanadin Mutuwar Fararen Hula A Mali

2021-01-07 10:07:35
Tababa Kan Harin Da Ya Yi sanadin Mutuwar Fararen Hula A Mali

A Mali, har yanzu ana ci gaba da tababa kan hakikanin abunda ya faru a tsakiyar kasar inda mutane kimanin 20 suka rasa rayukanusu sakamakon wani harin sama.

Rahotanni daga Malin dai, na cewa fararen hula da dama ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake kyautata zaton na sojojin Faransa ne na tawagar Barkhane a tsakiyar kasar Mali.

Mazauna da wasu kungiyoyin kauyen Bounti, sun shaida wa kamfanin dilancin labaren France-Presse, cewa sun fuskanci harin wani jirgin helikwabta, a ranar Lahadi data gabata wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 19 ciki har da yara.

Harin dai a cewar rahotanni, an kai shi kan wasu masu taron bikin aure.

Saidai faransa ta bakin rundinar sojinta, ta musanta labarin tana mai cewa harin data kaddamar ta kai shi ne kan gomman mayakan dake ikirari da sunan jihadi, kuma tana da tabbaci da kuma yakini kan hakan, saboda ta jima da take bibiyar gungun ‘yan ta’addan data kai wa hari.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!