AfCFTA Za Ta Kara Karfin Tattalin Arzikin Afirka Na Yaki Da COVID-19

2021-01-07 10:04:52
AfCFTA Za Ta Kara Karfin Tattalin Arzikin Afirka Na Yaki Da COVID-19

Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA), ta ce yarjejeniyar cinikayya marar shinge ta Afrika za ta kara karfin tattalin nahiyar na yaki da annobar korona.

Jami’in tsara manufofin hukumar, David Luke, ya bayyana cewa, yarjejeniyar cinikayya maras shige ta Afirka (AfCFTA), za ta iya kara karfin tattalin arzikin Afirka, koda duniya za ta iya fuskantar wata matsala nan gaba, kamar annobar COVID-19 da ake fama da ita yanzu.

Cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, masanin ya bayyana cewa, cinikaya tsakanin kasashen nahiyar, za ta taimaka wajen magance duk wata irin matsala da duniya ka iya tsintar kanta, kamar annobar COVID-19 da ta kara fito da raunin kasashen nahiyar na dogora kan abokan cinikayyarsu a sauran sassan duniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!