​Iran Ta Ce Tana Da Kwakwaran Shaidu Na Cewa Isra’ila Tana Da Hannu Wajen Kissan Fakhrizadeh

2021-01-06 22:54:52
​Iran Ta Ce Tana Da Kwakwaran Shaidu Na Cewa Isra’ila Tana Da Hannu Wajen Kissan Fakhrizadeh

Ministan tsaron kasar Iran Burgediya Janar Amir Hatami ya bayyana cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana da hannu dumu-dumi a kissan masanin fasahar Nukliya ta kasar wanda aka kashe a watan Nuwamban da ya gabata. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami yana fadar haka a yau Laraba ya kuma kara da cewa ya aika da wasiku zuwa ga tokororinsa a wasu kasashe 60 na duniya sangane da hakan.

A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata ne aka kashe Dr Mehsen Fakhrizadeh a wani wuri a wajen birnin Tehran a lokacinda yake kan hanyarsa ta zuwa wajen aikinsa.

Dr Fakhrizadeh dais hi ne mataimakin ministan tsaron kasar Iran sannan shugaban cibiyar bincike na ma’aikatar tsaron kasar. Ya taka rawar a zo a gani a ayyukan ci gaban kasar a bangarorin tsaro da kiwon lafiya da dama.

Kuma shi ne masanin fasahar Nukliya na kasar Iran wanda firai ministan HKI ya kama sunansa a wani jawabin da yay i a shekara 2018.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!