Iraki: An Kama Wani Daga Cikin Shuwagabannin Mayakan Daesh A Kudancin Bagdaza
2021-01-06 22:50:58

Jami’an tsaro a kasar Iraki sun bada sanarwan kama wani babba daga cikin shuwagabannin kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kudancin birnin Bagdaza. Kamfanin dillancin labaran Almalumah na kasar ta Iraki ya bayyana cewa, kafin haka dai shugaban ‘yan ta’addan ya kasance mufti a yankin Furat na lardin Ambar a lokacinda kungiyarsa take mamaye da yankin.
Bayan an dawo da ikon kwamnati a yankin sai ya
fice daga lardin ya dawo kudancin birnin Bagdaza, saboda kaucewa jami’an tsaron
kasar.
Tun shekara 2017 ne jami’an tsaron kasar Iraki
suka kawo karshen ikon gwamnatin Daesh amma har yanzun daga lokaci zuwa lokaci
sukan kai hare-haren ta’addanci a cikin kasar.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!