​An Zabi Wani Ba’irane A Matsayin Wanda Ya Fi Saka Kwallo A Wasan Kwallon Kwando A Turai

2021-01-06 22:35:54
​An Zabi Wani Ba’irane A Matsayin Wanda Ya Fi Saka Kwallo A Wasan Kwallon Kwando A Turai

Dan wasan kwallon Kwando daga kasar Iran, kuma wanda yake wasa ga kungiyar wasan Kwallon Kwando ta Skra Belchatow a Turai ya na daga cikin wadanda aka zaba a cikin kwararrun ‘yan wasan kwallon Kwando a fagen kai hari.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasare Iran ya bayyana cewa Milad Ibadii-Poor ya sami kyautar lambar yabo da dan wasa mafi kai hare-hare a gasar wasannin kwallon Kwando na shekarar da ta gabata ne bayan an kammala gasar.

Abidipoor yana wasa wa wata kungiyar kwallon Kwando na kasar Polanda ne, kuma ya sami amincewar kashi 68.8% na alkalan zaben zababbun ‘yan wasan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!