Sheikh Zakzaky: Hajj Qasim Yayi Gagarumin Kokari Wajen Hada Kan Musulmin Duniya

Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana cewar Janar Qasim Sulaimani, tsohon kwamandan rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran da yayi shahada ya taka gagarumar rawa da kuma yin kokari wajen tabbatar da hadin kan al’ummar musulmi na duniya.
Sheikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a yayin da wasu na kurkusa da
shi da kuma wasu membobin ofishinsa suka kai masa ziyara a inda ake tsare da
shi, inda yayin da yake Magana kan zagayowar shekara guda da shahadar Janar
Qasim Sulaimanin da kuma Abu Mahdi
al-Muhandis yayi addu’ar samun girma matsayi da daukaka ga wadannan manyan
shahidai guda biyu yana mai cewa lalle Janar Sulaimanin ya taka gagarumar rawa
wajen ganin an samu hadin kai tsakanin ‘yan Shi’a da Sunna.
Kafar watsa labaran Islam Times ta jiyo daya daga cikin wadanda
suka halarci wanann ganawar yana fadin cewa: A yayin wannan ganawar da ta
gudana a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, Sheikh Zakzaky ya bayyana
wadannan shahidai biyu a matsayin gwarazan sansanin gwagwarmaya yana mai addu’ar
Allah Ya sanya su karkashin inuwar Imamai tsarkaka (a.s).
Har ila yau dan harkar Musulunci ta Nijeriya da ya halarci wannan
ganawar ya bayyana cewar duk kuwa da cewa jami’an tsaron Nijeriya suna a wajen
wannan ganawar amma hakan bai haka
Sheikh Zakzaky ya bayyana matsayarsa kan Shahid Qasim Sulaimanin da kuma
jinjina masa kan irin rawar da ya taka wajen tabbatar da hadin kai tsakanin al’ummar
musulmi ba.
Haka nan kuma Sheikh Zakzaky ya bayyana farin cikinsa da yadda ‘yan
kungiyar harkar musulunci ta Nijeriyan suka gudanar da tarurrukan da suka shafi
zagayowar shekara guda da shahadar Janar Qasim Sulaimanin a garuruwa
daban-daban na Nijeriya din.
A kwanakin baya ne dai mabiya Sheikh Zakzaky din a Kano karkashin jagorancin wakilinsa a Kano Dakta Sunusi Abdulkadir suka gudanar da taron tunawa da shekara guda da shahadar Janar Qasim Sulaimani da shahid Abu Mahdi al-Muhandis a garin na Kano lamarin da ya samu halartar jama’a da yawan gaske.