Kasashen OPEC, Sun Amince Kara Yawan Man Da Suke Hakowa
2021-01-06 13:22:20

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, (OPEC) sun amince su kara yawan man da suke hakowa da ganga dubu 500 kowace rana a watan Janairu.
Ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ce yayin taronta karo na 13 tsakanin 'yan OPEC da kuma ministocin kasashen da ba mamba ba, wanda aka yi a birnin Vienna na kasar Austria ranar Talata.
Farashin man fetur dai ya yi
mummunar faduwa a shekara 2020 sakamakon annobar korona, wadda ta hana
hada-hadar kasuwanci a fadin duniya.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!