Tattalin Arzikin Duniya Zai Bunkasa Da Kaso 4 Cikin 100 A Bana

2021-01-06 13:19:56
Tattalin Arzikin Duniya Zai Bunkasa Da Kaso 4 Cikin 100 A Bana

Bankin duniya ya fitar da wani sabon hasashe game da makomar tattalin arzikin duniya na nuna cewa, tattalin arzikin duniya ya kama hanyar bunkasa da kaso 4 cikin 100 a shekarar 2021.

Shugaban bankin, David Malpass, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, da alamun tattalin arzikin duniya yana farfadowa daga daga durkushewar da ya yi sanadin annobar korona.

M. Malpass ya ce, koda yake tattalin arzikin duniya yana farfadowa, bayan koma bayan da ya fuskata na kaso 4.3 a shekarar 2020, annobar COVID-19 ta jefa miliyoyin mutane cikin kangin talauci, kuma hakan na iya nakasa harkokin tattalin arziki na dogon lokaci.

Wannan ne a cewa M. Malpass, akwai bukatar harkar zuba jari ta runguma yadda tattalin arzikin ya farfado, wanda zai zamo muhimmin mataki na kara farfado da tattalin arzikin duniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!