​Kamalvandi: Iran Za Ta Iya Tace Sanadarin Uranium Daga Kashi 40% Zuwa 60%

2021-01-06 10:17:02
​Kamalvandi: Iran Za Ta Iya Tace Sanadarin Uranium Daga Kashi 40% Zuwa 60%

Kakakin hukumar makamshin nukiliya ta kasar Iran ya bayyana cewa, kasar za ta iya tace daga kashi 40% zuwa kashi 60%.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yammacin jiya Talata a birnin Tehran, kakakin hukumar makamshin nukiliya ta kasar Iran Behruz Kamalvandi ya bayyana cewa, a halin yanzu sun fara aikin tace sanadarin uranium kashi 20% kamar yadda suka sanar.

Ya ce; daukar wannan mataki ya zo ne sakamakon kasa cika alkawullan da kasashen yammacin turai suka dauka dangane da yarjejeniyar nukiliya da aka rattaba hannu a kanta tare da Iran.

Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Iran tana ton 4 na tataccen sanadarin uranium a cibiyoyinta na nukiliya, kuma za ta rika samar da kilo 50 a kowane wata daga yanzu, inda yawan tataccen uranium din zai kai ton 10 daga nan zuwa shekara guda.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin ayyukan da Iran ta fara ahalin yanzu suna gudana ne bisa sanya ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Sai dai a nasu bangaren kasashen yammacin turai da Isra’ila, sun nuna matukar damuwa dangane da wannan mataki da Iran ta dauka, inda suke ganin cewa tace kashi 20% na uranium zai iya baiwa Iran damar kera manyan makamai na nukiliya, yayin da ita kuma Iran din ta sake jaddada cewa shirin nata na ayyukan farar hula ne.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!