​Najeriya: Gwamnati Za Ta Shigo Da Allurar Rigafin Corona Dubu 100 A Cikin Wannan Wata

2021-01-06 09:41:44
​Najeriya: Gwamnati Za Ta Shigo Da Allurar Rigafin Corona Dubu 100 A Cikin Wannan Wata

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Pfizer da BioNTech 100,000 a karshen wannan wata na Janairu.

Shugaban hukumar kiwon lafiya matakin farko na ƙasa, NPHCDA Faisal Shuaib ya sanar da haka ranar jiya Talata a yayin ganawa da kwamitin PTF ya yi da manema labarai a Abuja.

Shuaib ya ce kamfanin COVAX wanda ya dauki nauyin shigo da magungunan zai shigo da kwalaben maganin 100,000 sannan daga baya kamfanin zai kara shigowa da kwalabe miliyan 42 na maganin a matsayin gudunmawa ga Najeriya daga kamfanonin GAVI da vaccine alliance.

Ya ce maganin rigakafin guda miliyan 42 din da za a shigo da su, zai kunshi ire-iren magungunan rigakafin cutar da hukumomin kiwon lafiya na duniya suka amince da su, sannan kuma zai isa ayi wa akalla kashi 20% mutanen Najeriya allurar rigakafin.

Idan ba a manta ba gwamnati ta kafa kwamitin mutum 18 wanda za su tabbatar Najeriya ta samu maganin rigakafin cutar korona da zaran hukumomin lafiya sun amince da shi.

Sai dai wasu kwararru a bangaren kiwon lafiya na ganin cewa, da wuya Najeriya ta fara yi wa mutane allurar rigakafi a watan Janairu ganin yadda kasashen duniya da dama suke kan layin neman maganin domin mutanen su.

Haka nan kuma kwararrun suna ganin cewa, a halin yanzu haka Najeriya ba ta da wurin ajiyar wadannan magunguna ko da an shigo da su kasar.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!