​Rasha: Amurka Ce Ummul Haba’isin Komawar Iran Ga Aikin Tace Uranium Kashi 20%

2021-01-06 09:13:25
​Rasha: Amurka Ce Ummul Haba’isin Komawar Iran Ga Aikin Tace Uranium Kashi 20%

Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana matakin da Iran ta dauka na fara aikin tace sanadarin uranium kashi 20% da cewa ba shi da wata alaka da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, wakilin kasar Rasha hukumar makamshin nukiliya ta duniya Mikhail Ulyanov ya bayyana cewa, irin matakan da Amurka ta dauka dangane shirin Iran na nukiliya ne, ya sanya Iran din daukar matakin komawa ga tace uranium kashi 20% a shirinta na nukiliya.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, babu wata alaka tsakanin matakin da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, tare da jaddada cewa komawar dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zuwa ga yin aiki da ita ne zai kawo karshen wannan dambarwa.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar Rasha ta dora alhakin dukaknin matsalolin da aka samu dangane da wannan yarjejeniya a kan Amurka, sakamakon ficewar da gwamnatin Trump ta yi daga cikin wannan yarjejeniya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!