Ndume: Sojojin Najeriya Sun Karbi Makudan Kudade Domin Tabbatar Da Tsaro A Shekarar 2021

Shugaban Kwamitin Sojoji na
Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa babu sauran wani uziri da
rundunar sojin Najeriya za ta bayar, domin an ba su komai a wadace, da kuma isassun
makudan kudade domin magance matsalar Boko Haram a cikin 2021.
A rahoton da jaridar Premium Times ta bayar, Ndume ya bayyana cewa sojojin
Najeriya sun samu duk wata bukatar da suka nema a biya masu ta fannin sayen
manyan makamai da lodin sauran kayan artabu, domin magance matsalar Boko Haram
da ’yan bindiga a Najeriya.
Wannan bayani na Sanata Ndume ya zo
ne kusan mako daya bayan Babban Hafsan Hafsoshin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai
ya bayyana cewa, “sojoji za su kunyata Boko Haram cikin 2021.”
Ndume ya kara cewa gwamntin tarayya
ta amince da dukkan bukatun da mahukuntan tsaro na soja su ka mika domin
magance ta’addanci da ’yan bindiga a kasar, domin kuwa majalisa ma cewa ta yi a
gaggauta damka wa sojoji dukkan makudan kudaden da su ka bukata.
Ya ce “Kasafin Kudin Sojoji na 2021 tun daga
albashi da komai, ya kai naira bilyan 500, a Shekarar da ta gabata naira bilyan 75 aka
kashe wa Operation Lafiya Dole kadai. Amma wannan shekarar shugabannin sojojin
sun yi korafi, sai aka yi masu kari zuwa naira bilyan 100.’’