Rundunar Sojin Iran Sun Fara Gagarumin Atisayen Jiragen Sama Marasa Matuka Na Yaki

2021-01-05 21:27:41
Rundunar Sojin Iran Sun Fara Gagarumin Atisayen Jiragen Sama Marasa Matuka Na Yaki

Rundunar sojin ƙasar Iran ta fara gudanar da wani gagarumin atisayen jiragen saman yaƙi marasa matuƙa mallakin dakarun ƙasa, na ruwa da na sama na rundunar sojin Jahmuriyar Musulunci ta Iran ɗin a yau ɗin nan Talata.

Rahotanni sun ce shi dai wannan atisayen na kwanaki biyu ana gudanar da shi ne lardin Semnan da ke arewacin ƙasar ta Iran kuma ya ƙumshi ɗaruruwan jiragen saman yaƙi marasa matuƙa ne da ƙwararrun ƙasar suka ƙera su.

Yayin da ya ke ƙarin haske dangane da atisayen, mataimakin kwamandan ɓangaren ayyuka na rundunar sojin ta Iran, Rear Admiral Mahmoud Mousavi ya bayyana cewar a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana daga cikin ƙasashen duniya da suke da ƙarfin gaske a ɓangaren jiragen saman yaƙi marasa matuƙa.

Admiral Mousavi ya ƙara da cewa: A yayin wannan atisayen, jiragen saman yaƙi marasa matuƙa daban-daban na sojojin ƙasa, ruwa da kuma sama za su gudanar da ayyuka daban-daban da aka tsara musu don gwada irin ƙarfin da suke da su.

Kwamandan ya ƙara da cewa a yayin atisayen dai za a gwada yadda ake kai farmaƙi daga nesa da waɗannan jiragen da kuma dabarun ganowa da kuma kakkaɓo jirage da makamai masu linzami da aka harbo bugu da ƙari kan tarwatsa wajaje da sansanonin maƙiya.

A shekarun baya-bayan nan dai Iran ta ƙera makamai da kuma irin waɗannan jiragen saman yaƙi da nufin kare kanta daga hare-hare da kuma barazanar maƙiya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!