An Sake Karin Kuɗin Wutar Lantarki A Nijeriya Da Kashi 50 Cikin Dari

2021-01-05 21:24:07
An Sake Karin Kuɗin Wutar Lantarki A Nijeriya Da Kashi 50 Cikin Dari

Rahotanni daga Nijeriya sun ce gwamnatin ƙasar ta amince da sake ƙara kuɗin wutar lantarki da masu amfani da ita za su biya a ƙasar lamarin da ya sake janyo kace-nace a ƙasar.

Rahotanni daga ƙasar sun bayyana cewar Hukumar kula da farashin wutar lantarki a Najeriya (wato Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta amince da fara aiki da wani sabon ƙarin kuɗin wutar da kashi fiye da 50 cikin 100.

Hukumar ta ce ta yi la'akari ne da tashin farashin kaya na kashi 14.9 cikin 100 a watan Nuwamba, da faɗuwar darajar naira da ƙarfin samar da wutar lantarkin, kafin ta yi ƙarin kuɗin.

Wannan na zuwa ne wata biyu kacal da yin irin wannan ƙarin kuma na yanzu zai shafe na watan Nuwamba da aka yi.

Wasu kafafen watsa labarai dai sun ce ƙarin kuɗin zai shafi kowa da kowa saɓanin wanda aka yi a watan Nuwamban da ya gabata ɗin, sai dai hukumar ta musanta hakan tana cewa ƙarin kuɗin wutar da ta yi bai shafi waɗanda ke shan wutar a matakin D da E ba waɗanda suke samun lantarki ne ta ƙasa da awa 12 a kowace rana kuma hukumar ta ce ƙarin na kashi 50 cikin 100 bai shafe su ba.

Al’ummar Nijeriya ɗin dai suna ƙorafi ainun dangane da wannan mataki musamma bisa la’akari da irin halin da ake ciki na ƙumci da rashi a ƙasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!