Iran Ta Mika Sunayen Wasu Jami’an Amurka 48, Ciki Har da Trump, Ga Interpol Saboda Kisan Sulaimani

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar wa hukumar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa Interpol sunayen wasu jami’an ƙasar Amurka su 48 da take so a kamo mata su saboda hannun da suke da shi cikin kisan gillan da aka yi wa kwamandan rundunar Qudus na ƙasar, Laftanar Janar Qasim Sulaimani.
Kakakin Ma’aikatar shari’a ta ƙasar Iran
ɗin, Gholamhossein Esmaili ne ya sanar da hakan a wata ganawa da yayi da manema
labarai a yau ɗin nan Talata inda ya ce tuni Iran ta gabatar da buƙatar a kamo
mata shugaban Amurkan, Donald Trump da wasu manyan jami’an ƙasar su 47 da suke
da hannu cikin kisan gillan da sojojin Amurkan suka yi wa Janar Qasim
Sulaimanin.
Mr. Esmaili ya ƙara da cewa Jamhuriyar Musulunci
ta Iran da gaske take yi wajen bin diddigin waɗanda suke da hannu cikin wannan ɗanyen
aikin da kuma hukunta su.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Iran ta
gabatar da sammaci na ƙasa da ƙasa wajen kamo Trump da wasu jami’an Amurkan da
suke da hannu cikin wannan danyen aikin.
A watan Yunin shekarar da ta gabata,
babban mai shigar da ƙara na birnin Tehran Ali Alqasimehr ya fitar da sammacin
kamo Trump da jami’an Amurkan don su fuskanci shari’ar kisan gillan da kuma
ayyukan ta’addanci.
A ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne dai
sojojin Amurkan bisa umurnin shugaba Trump suka kai hari kan motar da take ɗauke
da Shahid Qasim Sulaimanin a kusa da filin jirgin saman Bagadaza na ƙasar Iraƙi
inda yayi shahada.
Jami’an Iran dai sun bayyana cewa lalle za su ɗau fansa jinin Janar ɗin da aka zubar kamar yadda kuma suka ce za su ci gaba da neman dukkanin waɗanda suke da hannu cikin wannan ɗanyen aiki har sai an zartar musu da hukuncin da yayi daidai da su.