Sama Da Mutane 20 Ne Aka Kashe A Wani Hari Da Aka Kai Gabashin Demokradiyyar Kongo

2021-01-05 21:09:15
Sama Da Mutane 20 Ne Aka Kashe A Wani Hari Da Aka Kai Gabashin Demokradiyyar Kongo

Alal aƙalla mutane 21 ne aka ce sun rasa rayukansu a wani ƙauye da ke gabashin Demokraɗiyyar Kongo a wani hari da ake tsammanin masu tsaurin ra’ayin addini ne suka kai shi yankin kamar yadda jami’an yankin suka sanar a yau Talata.

Wata majiyar tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta ke kasar DRC ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa a yammacin jiya Litinin ne masu ɗauke da makamin suka ƙaddamar da wannan harin a ƙauyen Mwenda da bindigogi da adduna inda suka kashe mutane 21 baya ga waɗanda suka raunana.

Babban jami’in yankin dai ya ɗora alhakin wannan hari ga ƙungiyar nan ta Allied Democratic Forces (ADF), wata ƙungiya mai ikirarin kare Musulunci a ƙasar Uganda.

Ita dai wannan kungiyar wacce take zaune a kasar DRC tun shekarar 1995, ta kasance tana gudanar da ayyukanta na kai hare-hare da kashe jama’a a yankin kamar yadda jami’an suka faɗi.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!