‘Yan Wasa Da Jami’ai 40 Ne Suka Kamu Da Cutar COVID-19 A Gasar Premier Na Ingila

2021-01-05 21:04:43
‘Yan Wasa Da Jami’ai 40 Ne Suka Kamu Da Cutar COVID-19 A Gasar Premier Na Ingila

Hukumar gasar Premier League ta ƙasar Ingila sun sanar da cewa alal aƙalla ‘yan wasa da jami’an ƙungiyoyin kwallon ƙafa 40 ne suka kamu da cutar nan ta COVID-19 cikin ‘yan makonnin da suka gabata lamarin da ya ƙara irin fargabar da ake da ita.

Hukumar ta ce cikin ‘yan makonnin da suka gabata ta gudanar da gwaji kimanin 2,295 a kan ‘yan wasa da jami’an ƙungiyoyin kwallon ƙafa daban-daban inda tsakanin ranakun 28 ga watan Disamban da ta gabata zuwa 31 ga watan, an samu mutane 28 da suka kamu da cutar./

Har ila yau kuma hukumar tace an sake samun wasu 18 da suke da cutar a wani gwajin da aka gudanar.

Wannan yanayin dai ya ƙara sanya tsoro cikin zukatan ‘yan wasa da jami’an na su kan irin yadda ake samun ƙaruwar yaɗuwar cutar wacce ta haifar da hasarar gaske da ƙungiyoyin kwallon kafan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!