​Araqchi: Aikin Tace Uranimu Kashi 20% Da Iran Ta Fara Bai Saba Wa Yarjejeniyar Nukiliya Ba

2021-01-05 13:19:49
​Araqchi: Aikin Tace Uranimu Kashi 20% Da Iran Ta Fara Bai Saba Wa Yarjejeniyar Nukiliya Ba

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, aikin tace sanadarin uranium kashi 20% bai saba wa yarjejeniyar nukiliya da aka rattaba hannu a kanta tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba.

A zantawarsa ta tashar talabijin ta biyu ta kasar Iran a daren jiya, Abbas Araqchi ya bayyana cewa, matakin da Iran ta dauka na tace sanadarin uranium kashi 20% bai saba wa wata doka ta cikin kasa ko ta duniya ba.

Ya ce kamar kowace kasa ta duniya, kasar Iran tana da hakkin ta amfana da fasahar nukiliya domin ayyuka na farar hula da ci gaban kasarta da al’ummarta, kuma wannan aiki an fara shi ne a gaban wakilan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kuma duk abin da ake yi agaban idanunsu yake wakana.

Dangane da bayanin da kungiyar tarayyar turai ta fitar da cewa Iran sabon matakain na Iran ya saba wa yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da kan shirinta na nukiliya, Araqchi ya ce kasashen tarayyar turai su sake koma su karanta abin da yarjejeniyar ta kunsa da kyau.

Ya ce shashi na 36 na yarjjeniyar ya yarje wa Iran da ta kara yawan tataccen sanadarin uranium da take bukata, matukar dai kasashen da suke cikin yarjejeniyar ba su samar mata da shi ba kamar yadda aka cimma matsaya, ya ce kuma abin da ya faru kenan, su ba su cika alkawalinsu na samar da shi, saboda haka Iran za ta samar da shi da kanta, kuam ba ta bukatar neman izin kowa kan hakan.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!