​Man United Za Ta Sayar Da Pogba Bayan Yaki Amincewa Da Sabon Kwantaragi

2021-01-05 12:18:05
​Man United Za Ta Sayar Da Pogba Bayan Yaki Amincewa Da Sabon Kwantaragi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta sayar da dan wasanta na tsakiya, Paul Pogba mai shekara 27 a duniya a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya tabbatar da cewa ba zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ba a kungiyar.

Wannan na zuwa ne duk da cewa a ‘yan kwanakin nan tauraruwar dan wasan tana haskawa inda a wasan da kungiyar ta fafata na karshe da kungiyar Aston Billa ya samu kyautar dan wasan da yafi nuna bajinta a wasan da suka samu nasara daci 2-1 a filin wasa na Old Trafford

Har wa yau, Manachester United din ta rasa abin yi game da dan wasan Ingila da Dortmund, Jadon Sancho mai shekara 20, yayin da Ole Gunnar Solskjaer ya fi son Erling Braut Haaland na Dortmund din mai shekara 20 shi ma.

Sai dai abu ne mai wahala kungiyar Dortmund ta sayar da dan wasa Haaland kuma dole ne kungiyar ta dage akan dan wasan duba da yadda manyan kungiyoyi irinsu Real Madrid da Barcelona da Bayern Munich suke bibiyar matashin dan wasan dan kasar Norway.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!