CRA : Touadera Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Gagarimin Rinjaye

2021-01-05 09:58:23
CRA : Touadera Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Gagarimin Rinjaye

Shugaba mai barin gado na jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra, ya lashe zaben shugaban kasar da gagarimin rinjaye tun a zagayen farko.

Bisa sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta sanar a jiya Litinin, shugaba Touadera ya samu kaso 53,92 na daukacin kuri’un da aka kada yayin zaben da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata.

Hukumar zaben ta (ANE) ta ce, babban abokin takarar shugaba Toaudera, kana tsohon firaministan kasar, Anicet Georges Dologuele ne ya zo na biyu, bayan ya samu kaso 21,01 na dukkan kuri’un da aka kada.

Saidai Mista Dologuele, na mai kalubalanci sakamakon zaben wanda a cewarsa yana cike da kura kurai da kuma magudi.

Sai zuwa nan da ranar 19 ga watan Janairun nan ne kotun kundin tsarin mulkin kasar, za ta sanar da sakamakon zaben na dindindin.

A ranar 27 ga watan Disamban da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasa gami dana ‘yan majalisar dokoki a jamhuriyar Afrika ta tsakiya dake fama da rikici na ‘yan tawaye da gwamnatin kasar ke zargi da samun goyan bayan tsohon shugaban kasar Francois Bozize, wanda kotun kolin kasar ta yi watsi da takararsa a zaben.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!