Gidauniyar ECW Ta Alkawarta Baiwa Yankin Sahel Tallafin Dala Miliyan 33

2021-01-05 09:47:59
Gidauniyar ECW Ta Alkawarta Baiwa Yankin Sahel Tallafin Dala Miliyan 33

Shirin nan na Education Cannot Wait (ECW) dake gwagwarmayar samar da ilimi, ya sanar da samar da tallafin dala miliyan 33.3, don magance matsalar kiwon lafiya da jin kai da ake fama da su a kasashen Burkina Faso, da Mali da Nijar dake tsakiyar yankin Sahel.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, asusun na ECW ya bayyana cewa, sabbin shirye-shiryen da za a gudanar a kasashen uku, za su hallara duk kan masu ruwa da tsaki a harkokin jin kan bil-Adama da raya kasa, inda za su samar da ilimi mai inganci ga yara da matasan da aka bar su a baya a yankin.

Za dai a kwashe tsawon shekaru uku ne ana gudanar da shirye-shiryen, inda ake fatan kashe karin dala miliyan 117.8, da za a samar tsakanin abokan hulda na kasa da na duniya, da sassa masu zaman kansu da manyan masu bayar da gudummawa.

Yara mata dai na daga cikin wadannan matsaloli suka fi shafa.

Za a raba tallafin ne daidai wa daida tsakanin kasashen uku, inda kowa ce kasa, za ta samu dala miliyan 11.1.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!