Falasdinu:Ma’aikatar Kiwon Lafiya Ta Nuna Damuwarta Da Yaduwar Korona A Cikin Gidajen Yari Isra’ila

2021-01-04 21:25:54
Falasdinu:Ma’aikatar Kiwon Lafiya Ta Nuna Damuwarta Da Yaduwar Korona A Cikin Gidajen Yari Isra’ila

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta bayyana damuwarta da yadda cutar korona take yaduwa a cikin gidajen yarin haramtacciyar kasar Isar’ila (HKI) musamman a gidajen yarin da, ba zai yu a bada tazara tsakanin fursinoni ba.


Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mai Al-Kaila ministan kiwon lafiya na Falasdinawa tana fadar haka a jiya Lahadi.

Al-kaila ta kara da cewa, hukumomin yahudawan Isra’ila ba sa kula da kiwon lafiyan fursinoni falasdinawa wadanda suke tsare da su a yankunansu da suke mamaye da su. Wannan ya sa akwai yiyuwan cutar ta yadu da gaggawa a tsakanin falasdinawa nan gaba.

Daga karshe ministan ta ce zata dorawa hukumomin HKI duk abinda ya sami falasdinawa saboda halin ko in kula da take nunawa dangane da wannan lamarin. Wannan, duk tare da gargadin da ma’aikatar da kuma wasu cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban suke yi wa yahudawan.

019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!