Iran: An Shiga Mataki Na Biyu Na Gwajin Allurar Rigakafin Cutar Korona

2021-01-04 21:21:43
Iran: An Shiga Mataki Na Biyu Na Gwajin Allurar Rigakafin Cutar Korona

An fara marhala ta biyu na gwajin alluran riga kafin cutar korona a nan Iran a safiyar yau Litinin. Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta nakalto Hamid Husaini shugaban cibiyar gwaje-gweje na asbitin koyarwa ta Jami’ar Tehran yana fadar haka.

Husaini ya kara da cewa gwajin marhalar farko ta fitar da sakamako mai kyau, inda dukkan ‘yan sa kai wadanda aka yiwa alluran suke cikin koshin lafiya.

Labarin ya kara da cewa za’a kammala aikin gwaje-gwajen ne a cikin watanni biyu, kuma za’a yi wa mutane 56 alluran a marhaloli daban daban a cikin matakan gwajin.

Alluran riga kafin cutar ta korona mai suna “COVIRAN BARAKAT” ya shiga marhala ta gwaji kan mutane ne a ranar 29 ga watan Dicemban da ya gabata.


019

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!